Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin: raya hulda a tsakaninta da Amurka, buri ne na jama'ar kasashen 2
2019-07-01 19:42:19        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana yau Litinin 1 ga watan Yuli a nan Beijing cewa, raya huldar da ke tsakanin kasashen Sin da Amurka, buri ne na jama'ar kasashen 2, lamarin da kasashen duniya suke sa ran gani. Kasashen 2 suna da moriyar bai daya a sassa daban daban, suna kuma hada hannu a fannoni da yawa. Ya ce ya kamata su magance tayar da rikici ga juna. Kana kamata ya yi su sa wa juna kaimi domin samun ci gaba tare.

Rahotanni sun ce, kwararru kimanin 80 na Amurka masu ilmin batun Asiya, sun shirya aika wa shugaban Amurka, da majalisar dokokin kasar wata wasika a fili, inda suka ce, wasu matakan da Amurka ta dauka suna kara raunana huldar da ke tsakaninta da Sin. Yadda Amurka ta mayar da Sin kamar abokiyar gaba, da kuma raba tattalin arzikin kasar Sin daga tattalin arzikin duniya, ya bata sunan Amurka a duniya, tare da lahanta moriyar dukkan kasashen duniya ta fuskar tattalin arziki. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China