![]() |
|
2019-07-09 21:19:06 cri |
Geng wanda ya bayyana hakan a Talatar nan yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa a nan birnin Beijing, ya ce, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta martaba manufar kasar Sin daya tak a duniya da sanarwowi guda uku game da alakar Sin da Amurka, ta hanzarta janye shirinta na sayarwa yankin makamai da ma huldar soja tsakaninta da yankin na Taiwan don kaucewa kara dagula alaka tsakanin kasashen biyu, da samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin Taiwan.
Geng ya yi wadannan kalamai ne, yayin da ya ke mayar da martani, ga shirin Amurka na sayarwa yankin na Taiwan makamai da darajarsu ta kai biliyan 2.2, ciki har da tankokin yaki samfurin M1A2 Abrams da na'urorin kakkabo makamai masu linzami.
A wannan rana kuma, memban hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin, kana direktan ofishin kula da harkokin wajen kwamitin tsakiya na jam'iyyar Yang Jiechi, da kakakin ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na majalisar gudanarwar kasar Ma Xiaoguang su ma sun nuna adawa da shirin Amurka na sayar wa yankin Taiwan makamai.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China