Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: Kada wasu su daidaita huldar da ke tsakanin Sin da Amurka da tunaninsu tare da yin kuskuren fahimtar yanayi
2019-07-04 19:55:52        cri

A jiya Laraba ne jaridar "The Washington Post" ta kasar Amurka, ta wallafi wani sakon da mutane daga sassa daban daban na kasar suka aikewa shugaban kasar, da kuma majalissun dokokin kasar.

A yau Alhamis kuma, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya nuna amincewa da sakon bisa yadda ta kalli yanayin duniya bisa sanin ya kamata. Jami'in Sin ya kuma jaddada cewa, rikici da kuma sabani, ba sa iya wakiltar huldar da ke tsakanin Sin da Amurka. Ya kuma yi imanin cewa, tabbas za a iya tinkarar huldar da ke tsakanin Sin da Amurka bisa sanin ya kamata, a maimakon nuna taurin kai, da tsattsauran ra'ayi, da kuma bin manufar "cin moriya da faduwar wani".

A ranar 3 ga wata ne, jaridar "The Washington Post" ta wallafa wani sakon da aka aikewa shugaba Donald Trump, da majalissun dokokin kasar, wadda tsoffin manyan kusoshin kasar, da shahararrun masanan kasar suka rubuta, kana kwararru 95 daga sassan ilmi, harkokin diplomasiyya, aikin soja, da kasuwanci suka sanya hannu.

A cikin sakon, sun ce, mayar da kasar Sin tamkar abokiyar gaba, ba zai taimaka wajen cimma manufa ba. Wannan sakon da dimbin mutane suka sanya hannu domin nuna goyon baya, ta nuna cewa, babu wani ra'ayi daya da aka cimma kan goyon bayan manufofin nuna kiyayya ga kasar Sin. Har iya yau a cikin sakon, an gabatar da batutuwa 7 dangane da huldar da ake yi tsakanin Sin da Amurka. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China