Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta bayyana matukar damuwa game da karuwar hare-hare kan fararen hula a wuraren da ake rikici a Afrika
2019-07-25 13:15:44        cri
Tarayyar Afrika AU, ta bukaci bangarori masu rikici a nahiyar Afrika, su kare fararen hula da kadarorinsu daga hare-haren ababen fashewa.

Wata sanarwar da AU ta fitar a jiya, ta ce kwamitinta na sulhu ya sadaukar da taronsa na bayan bayan nan kan taken "Kare fararen hula daga amfani da makamai masu fashewa a yankunan a'lumma".

Da yake maraba da kokarin kasa da kasa kan inganta kare fararen hula da rage tasirin rikici a kansu da kadarorinsu kamar yadda dokar jin kai ta duniya ta tanada, kwamitin ya kuma bayyana matukar damuwa game da tabarbarewar jin kai saboda rikice-rikice da kuma yawan adadin jama'a wadanda hare-haren ke shafa.

Kwamitin ya ce hakan na faruwa ne saboda yadda ake amfani da ababen fashewa ba tare da wata manufa ba, wanda ya sabawa dokar kasa da kasa, musammam a yankunan birane. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China