Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya jaddada muhimmancin gudanar da ayyukan da za su inganta rayuwar alumma
2019-07-17 10:13:57        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada muhimmancin mayar da hankali kan akidar gudanar da ayyukan da za su inganta rayuwar al'umma da gina yankunan dake kan iyakar kasar daga arewa, zuwa yankuna masu kayatarwa.

Xi, wanda har ila shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS kana shugaban rundunar askarawar kasar, ya bayyana hakan ne, yayin rangadin gani da ido da ya kai yankin Mongoliya ta gida mai cin gashin kansa dake arewacin kasar Sin.

Yayin rangadin da ya kai daga ranar Litinin zuwa jiya Talata, shugaba Xi ya duba yadda aikin raya tattalin arziki da jin dadin jama'a da raya muhalli mai wayin kai ke gudana a yankin. Shugaba Xi ya kuma ba da umarnin aiwatar da gangamin JKS kan ilimi mai taken "A tsaya kan akidar kafa jam'iyya bil hakki da gaskiya" da zage damtse da ci da gamsar da jama'a, faranta musu rai da samar da tsaro. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China