Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi ya taya Michel murnar lashe zaben jagorancin majalissar zartaswar tarayyar Turai
2019-07-09 09:39:06        cri
A jiya Lahadi ne shugaba Xi Jinping, ya taya Charles Michel, murnar lashe zaben shugabancin majalissar zartaswar tarayyar Turai ta EU. Shugaba Xi ya ce ci gaban hulda tsakanin Sin da EU na kara samun tagomashi. Kaza lika dorewar wannan dangantaka ba kawai buri ne na sassan biyu ba, domin kuwa hakan zai kara inganta zaman lafiya da ci gaban duniya baki daya.

Shugaban na Sin ya ce kasarsa na goyon bayan Turai a fannin taka karin rawar gani a harkokin kasa da kasa. Ya ce yana matukar maida hankali ga ci gaban kawancen Sin da Turai, zai kuma yi hadin gwiwa da Mr. Michel wajen tabbatar da nasarar alakar sassan biyu, ta yadda za a kai ga wanzar da zaman lafiya da ci gaba, da kawo sauyi, da kara zamanantar da al'amura, ta yadda al'ummun Sin da na Turai za su kara amfana, kana akan ya haifar da ci gaba, da daidaito tsakanin sassan duniya gaba daya. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China