Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya gana da mai jiran gadon sarautar Abu Dhabi
2019-07-22 19:41:06        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da Yarima Mohammed bin Zayed Al Nahyan, mai jiran gadon sarautar Abu Dhabi, hedkwatar hadaddiyar daular Larabawa UAE.

Yayin ganawar, shugaba Xi ya ce, a lokacin da ake kokarin bunkasa duk duniya bai daya, hadin kai da samun moriya tare su ne ya kamata kasashen duniya su bi a lokacin da suke yin hadin gwiwa. Duk kasar da ta rufe kofarta ta kuma ware kanta daga dangi za ta yi illa ga muradunta. Ya ce, huldar Sin da Abu Dhabi ya zama abin koyi ga hadin kai bisa manyan tsare-tsare tsakanin yankuna daban-daban, da ma tsakanin mabambanta al'adu da kasashe daban-daban.

A nasa jawabi Mohammed bin Zayed Al Nahyan ya nuna cewa, Abu Dhabi ta jinjinawa kokarin da Sin take yi wajen kiyaye 'yancin al'ummar kananan kabilu da ingiza hadin kai da zaman lumana tsakanin al'ummomin dake cikin kasar, kana kasarsa tana fatan kara hadin kai da kasar Sin ta fuskar tsaro da dakile ayyukan masu tsattsauran ra'ayi, ciki hadda Sherqiy Türkistan, da kiyaye tsaron da kwanciyar hankalin yankin baki daya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China