Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Sin ya tattauna da takwaransa na kasar Turkiya
2019-07-03 10:44:57        cri

A jiya Talata ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna da takwaransa na kasar Turkiya Racep Tayyip Erdogan a dakin taruwar jama'a dake birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Yayin zantawar su, shugaba Xi ya yi alkawarin aiwatar da matakan bunkasa tsare-tsaren hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da Turkiya, ta yadda sassan biyu za su yi aiki tare domin inganta kawancen su yadda ya kamata.

Xi ya kara da cewa, Sin da Turkiya manyan kasuwanni ne masu tsowa kuma kasashe masu tasowa, don haka bunkasa alaka bisa manya tsare-tsare a tsakaninsu, abu ne mai muhimmanci.

Ya kuma yi kira ga sassan biyu, da su kara amincewa da juna ta fannin siyasa, da kulla alaka a fannin sadarwa, da mutunta muradun juna da manyan batutuwan da ke shafar kasashensu da 'yanci da cikakkun yankunansu, kana su martaba ginshikin siyasa dake shafar raya alakar kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare, ta yadda alakarsu za ta ci gaba bisa turbar da ta dace cikin lumana.

A nasa jawabin shugaba Erdogan ya ce, kasar Turkiya, za ta ci gaba da martaba manufar Kasar Sin daya tak a duniya, yana mai jaddada cewa, kabilu daban-daban suna zaune cikin lumana a yankin Xinjiang na Uygru mai cin gashin kansa na kasar Sin, saboda matakan da kasar Sin ta dauka., kuma Turkiya ba za ta bar wani mutum ya lalata alakarta da kasar Sin ba.

Ya kuma bayyana kudurinsa na kara mutunta juna ta fannin siyasa da karfafa alakar tsaro da kasar Sin wajen nuna adawa da masu tsattsauran ra'ayi. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China