Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ba amfani bangaren Amurka ya yi zargi kan ziyarar mataimakin babban sakataren MDD a Xinjiang
2019-06-17 19:56:22        cri
Mataimakin babban sakataren MDD dake kula da harkokin yaki da ta'addanci Vladimir Ivanovich Voronkov, ya ziyarci kasar Sin a tsakanin ranekun 13 zuwa 15 ga wata, inda ya kai ziyara a jihar Xinjiang, don fahimtar yadda ake yaki da ta'addanci, da kawar da tsattsauran ra'ayi a wurin. Game da haka, mataimakin sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Sullivan ya yi zargin cewa, wai ziyarar ba ta dace ba.

Game da wannan zargin, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya bayyana a yayin taron manema labaru da aka shirya a yau Litinin a nan birnin Beijing, cewa zargin da bangaren Amurka ya yi ba shi da amfani. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China