Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na fatan sassan kasa da kasa za su yi hadin gwiwa wajen yaki da ta'addanci
2019-07-10 10:09:53        cri
Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Ma Zhaoxu, ya ce abu ne mai muhimmanci ga kasashen duniya, su rika aiwatar da matakai na bai daya na yaki da ayyukan ta'addanci. Ma Zhaoxu ya yi wannan tsokaci ne a jiya Talata, yayin zaman muhawara na kwamitin tsaron MDD. Ya ce ta'addanci abokin gabar daukacin bil Adama ne, kuma ya zama wajibi a yi yaki da shi ba tare da raba kafa ba. Kaza lika a cewarsa, dole ne a bi ka'idojin MDD, da martaba iko da 'yancin mulkin kai, a duk kasashen da ake gudanar da wannan muhimmin aiki.

Jami'in ya kuma yi fatan dukkanin sassa a matakai na kasa da kasa, da na shiyya-shiyya, za su yi hadin gwiwa da juna, wajen yaki da ta'addanci, da kuma sauran munanan laifuka. Hakan a cewarsa zai yi nasara ne kawai, idan har an karfafa hadin gwiwa ta fannin musayar bayanan sirri, da na irin nasarori da ake samu, aka kuma yi aiki tukuru, wajen wanzar da yanayin zaman lafiya da tsaro a dukkanin sassan duniya.

Daga nan sai ya yi kira ga kasashen duniya, da su tallafawa kasashe masu tasowa da horo, na sanin makamar aiki a fannin yaki da ta'addanci. Ma Zhaoxu ya ce sassan da ke da bukatar tallafin sun hada da na tsaron kan iyakoki, da na shige da fice, da tsara dokokin dakile yaduwar miyagun kwayoyi, da kuma fannin shari'a.

A daya hannun kuma, ya bayyana bukatar da ake da ita, ta yaki da laifukan da ake aikatarwa ta yanar gizo, da sauran laifuka masu alaka da ta'addanci da manyan laifuka. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China