Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da Afirka sun jaddada muhimmancin samar da ci gaba domin inganta kare hakkin bil Adama
2019-07-10 10:02:25        cri
Sassan Sin da na nahiyar Afirka, sun yi hadin gwiwa wajen goyon bayan manufar rarraba ci gaba ga daukacin bil Adama, a matsayin wata muhimmiyar hanyar kare 'yancin dan Adam.

Sassan biyu sun bayyana hakan ne, a gefen taro na 41 na MDD game da kare hakkin dan Adam dake gudana a birnin Geneva. Taron dai majalissar kare hakkin bil Adama ta MDD, da hadin gwiwar ofishin jakadancin Sin, tare da tawagogin kasashen Afirka dake MDD ne suka shirya shi.

Da yake tsokaci game da hakan yayin bude taron, wakilin dindindin na kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva Chen Xu, ya ce neman ci gaba babban buri ne na daukacin bil Adama, ya kuma shafi dukkanin matakai na warware kalubalen dake fuskantar rayuwar al'umma.

Chen ya ce da yake tattalin arziki, da sabbin fasahohi ne ke haifar da ci gaba, ana iya ganin cewa akwai rashin daidaito game da yaduwar ci gaba, da rashin karadewar sa sassan duniya, da ma tsarin rabon sa. Ya ce ya kamata kasashen duniya su yi tunani mai zurfi, domin zakulo hanyoyin samar da ci gaba tare, su kuma sada karin mutane da ribar ci gaba, ta yadda hakan zai haifar da yanayi na kare hakkin bil Adama.

Shi kuwa a nasa tsokaci, jakadan tawagar Afirka ta kudu a MDDr Nozipho Mxakato-Diseko, cewa ya yi kare hakkin bil Adama batu ne da ya hade dukkanin sassan rayuwar bil Adama, kuma rashin karfin tattalin arziki na haifar da kalubale ga zamantakewa, da al'adu, da tsarin siyasar al'umma, don haka dai ko wane bangare na dogaro ga daya sashin.

Shi ma daraktan sashen habaka dunkulewa da bunkasa tsarin ci gaba, a taron karawa juna sani na MDD game da cinikayya da samar da ci gaba Richard Kozul-Wright, cewa ya yi karancin kudade na zama wani babban kalubale ga kasashen Afirka, kuma kasar Sin na taka muhimmiyar rawa a nahiyar, ta fuskar samar da kudaden aiwatar da ayyukan more rayuwa da samar da ci gaba. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China