Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sakatare Janar na MDD ya jinjinawa yarjejeniyar da bangarorin Sudan suka cimma
2019-07-06 15:07:31        cri
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya jinjinawa yarjejeniyar da aka cimma tsakanin kwamitin mulkin soji da bangaren adawa na kasar Sudan.

Mataimakin kakakin Sakatare Janar din Farhan Haq, ya ce Antonio Guterres ya taya Tarayyar Afrika da kasar Habasha murna, bisa rawar da suka taka na jagorantar tattaunawa tsakanin bangarorin Sudan, ya kuma yabawa kungiyar raya yankin gabashin Afrika bisa goyon bayan da ta bayar.

Kwamitin mulkin sojin da hadaddiyar kungiyar dake rajin samar da sauyi da 'yanci, sun aminci da kafa gwamnatin rikon kwarya da ta kunshi bangarorin biyu, wajen jagorantar kasar.

Sakatare Janar din ya karfafawa dukkan masu ruwa da tsaki gwiwar tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar cikin adalci kuma a kan lokaci tare da tafiya da kowa, da kuma warware sauran batutuwan dake ci musu tuwo a kwarya ta hanyar tattaunawa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China