Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan sanda: An sake yin garkuwa da mahaifiyar tsohon kociyan kungiyar kwallon kafan Najeriya
2019-07-16 09:22:47        cri

Mahaifiyar Samson Siasia, tsohon kociyan babbar kungiyar wasan kwallon kafan Najeriya, wasu 'yan bindiga a kudancin kasar sun yi garkuwa da ita a ranar Litinin, in ji hukumar 'yan sanda.

Matar mai suna, Beauty Ogere Siasia, 'yan bindigar sun yi awon gaba da ita ne a gidanta dake kauyen Odoni a karamar hukumar Sagbama dake jahar Bayelsa. Lamarin ya faru ne da misalin karfe biyun dare agogon kasar, in ji Butswat Asinim, kakakin hukumar 'yan sandan jahar.

Wannan shi ne karo na biyu da ake yin garkuwa da dattijuwar mai kimanin shekaru 76 a cikin shekaru 4. A watan Nuwambar shekarar 2015, 'yan bindiga sun yi garkuwa da ita kana suka sake ta bayan ta shafe kwanaki 12 a hannunsu.

Wasu majiyoyi a yankin sun ce an biya wasu kudaden da ba'a bayyana yawansu ba a matsayin kudaden fansa ga wadanda suka yi garkuwar da ita. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China