Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Nijeriya ya tafi taron AU inda zai rattaba hannu kan yarjejeniyar ciniki cikin 'yanci ta yankin
2019-07-06 16:24:28        cri
Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, zai bar birnin Abuja a yau Asabar, domin halartar taron Tarayyar Afrika, da za a yi gobe Lahadi a birnin Niamey na Niger.

Wata sanarwar da kakakin shugaban kasar Femi Adesina ya fitar, ta ce Muhammadu Buhari zai rattaba hannu kan yarjejeniyar ciniki mara shinge ta nahiyar, tare da halartar taron gama gari karo na 12 na tarayyar, kan yarjejeniyar da kuma taron farko na tsakiyar shekara na AU da kungiyoyin raya yankunan nahiyar.

Ana sa ran taron na AU ya kaddamar da tsarukan aiwatar da yarjejeniyar da ta kafa yankin ciniki mara shinge a nahiyar.

Tsarukan sun hada da ka'idojin asalin kayayyaki, manhajar cire haraji da manhajar sa ido da cire shingayen da ba na haraji ba, da tsarukan biyan kudi ta na'ura da na tantance kayayyaki da kuma manhajar nazarin yanayin cinikayyar nahiyar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China