Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dakarun Najeriya sun dakile hari a sansaninsu tare da hallaka mayakan Boko Haram masu yawa
2019-07-05 09:36:07        cri
Rundunar sojojin Najeriya ta sanar a jiya Alhamis cewa, dakarunta sun yi nasarar hallaka mayakan Boko Haram masu yawan gaske a lokacin da 'yan ta'addan suka yi yunkurin kaddamar da hari kan sansanin sojojin dake jahar Borno a shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Sojojin sun yi nasarar dakile harin ne a sansaninsu na runduna ta 212 dake Gajigana, a karamar hukumar Nganzai dake jahar Borno a daren ranar Laraba, inji Birgediya Janar Bulama Biu, babban jami'in dake jagorantar rundunar sojojin shiyyar.

Biu ya ce, dakarun sojojin tare da tallafin sojojin saman Najeriya sun yi hadin gwiwa wajen dakile harin da mayakan 'yan ta'adda na Boko Haram suka shirya kaddamarwa.

Mayakan Boko Haram cikin wasu tankokin yaki sun yi yunkurin kutsawa sansanin sojojin ne kwanaki biyu bayan sojojin sun dakile makamancin harin 'yan ta'addan a yankin Goniri dake jahar Yobe mai makwabtaka da jahar Borno.

Biu, wanda bai bayyana hakikanin adadin mayakan 'yan ta'addan da aka hallaka ba, ya ce sojojin sun yi nasarar kwace tankokin yaki biyu da kuma albarusai masu yawan gaske daga maharan.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China