Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwararren Najeriya: AfCTFA zata bunkasa ajandar hadin gwiwar raya masana'antu ta Sin da Afrika
2019-07-12 09:41:21        cri
Wani kwararren masanin dangantakar kasa da kasa daga Najeriya ya bayyana cewa, yarjejeniyar ciniki marar shinge ta Afrika (AfCFTA), wacce ta fara aiki bayan kaddamar da ita, Sin da Afrika za su ci moriyar dangantakar ta hanyar hadin gwiwar bunkasa masana'antu tsakanin bangarorin biyu.

Charles Onunaiju, daraktan cibiyar nazarin al'amurran kasar Sin dake Abuja, babban birnin Najeriya, ya bayyana a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, kasancewar dama akwai wani cikakken shirin hadin gwiwa da aka riga aka tsara, bangarorin biyu zasu yi hadin gwiwa da juna wajen cimma nasarar daga matsayin bunkasuwar masana'antu a Afrika.

"Ina tunanin akwai muhimman damammaki wadanda ake sa ran za su baiwa Afrika damar zama a sahun gaban ta fuskar cigaban masana'antu kasancewar an riga an rattaba hannu kan yarjejeniyar cinikin maras shingen a hukumance," inji kwararren. "Amma hakan ba zai tabbata ba, dole ne sai an dauki matakan tabbatarwa, ta hanyar tsare tsaren da suka dace."

A ranar Lahadi aka kaddamar da yarjejeniyar ta AfCFTA a lokacin babban taron kolin shugabanni da jami'an gwamnatocin mambobin kungiyar tarayyar Afrika (AU) karo na 12 wanda aka gudanar a Niamey, babban birnin jamhuriyar Nijer. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China