Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamaru da Nijeriya za su tattauna kan tsaron iyakokinsu
2019-07-05 10:06:12        cri
An bude taro na 7 na kwamitin kula da tsaron iyakokin Kamaru da Nijeriya a birnin Yaounden Kamaru a jiya Alhamis, inda aka jaddada bukatar karfafa tsaron kan iyakokin kasashen biyu.

Ministan kula da yankuna na Kamaru, Paul Atanga Nji, ya ce yanayin tsaro a kan iyakokin kasashen da ya fara samun ingantuwa, kwatsam ya fara zama abun damuwa, yana mai bayyana matsalar 'yan aware da hakar ma'adinai ta haramtacciyar hanya da safarar makamai, a matsayin manyan kalubale.

A cewar Brigadier Janar Emmanuel Ndagi na Nijeriya, za su ci gaba da mara baya ga kudurin Jamhuriyar Kamaru na karfafa tsaro a kan iyakokin da nufin sa ido da daukar matakan mayar da martani masu inganci.

An kafa kwamitin ne a shekarar 2012 a Nijeriya, da nufin karfafa tsaro a iyakokin kasashen biyu.(Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China