Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Akwai bukatar AU ta tsara matakan sanya mata cikin aikin warware rikici
2019-07-11 10:12:02        cri

Wakiliyar musamman ta mata, wanzar da zaman lafiya da tsaro a kungiyar tarayyar Afirka AU Bineta Diop, ta yi kira da a tsara tabbatattun manufofi a mataki na kasashe, game da shigar mata ayyukan wanzar da zaman lafiya da tsaro, ta yadda matan za su taka karin rawa a fannin warware rikice rikice.

Bineta Diop, ta bayyana hakan ne a jiya Laraba, yayin babban taron Afirka game yaki da ta'addanci, da kandagarkin ayyukan masu tsattsauran ra'ayi, wanda ya gudana a birnin Nairobin kasar Kenya. Ta ce kawo yanzu, kasashen Afirka 27 sun riga sun tsara nasu manufofi a wannan fanni.

Diop ta kara da cewa, ofishin ta na yayata wannan manufa ne, domin ganin an sanya batun wanzar da tsaro da zaman lafiya, cikin ajandojin samar da ci gaba na kasashen Afirka. Ta ce akwai bukatar majalisun dokokin kasashen su amince da wannan kuduri, domin shigar da shi cikin ayyukan zartaswa na gwamnatoci.

Daga nan sai ta bayyana fatan ta, na ganin mata sun samu kujerun jagoranci, a duk lokacin da ake aiwatar da shawarwari game da matakan warware tashe tashen hankula, da gina yanayi na zaman lafiya da lumana.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China