Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Afrika ta kudu za ta hukunta masu daukar ma'aikata 'yan ci rani
2019-07-11 10:28:54        cri

Mataimakin ministan harkokin cikin gidan Afrika ta kudu Njabulo Bheka ya ce, gwamnatin kasar za ta dauki tsattsauran hukunci kan duk wani kamfanin dake daukar baki 'yan kasashen waje wadanda suka zuwa kasar ba tare da cikakkun takardu ba domin su yi aiki.

"Za mu sanya kafar wando daya da dukkan masu daukar ma'aikata daga kasashen waje ba tare da samar da cikakkun takardu ba." Bheka ya bayyana hakan a lokacin gabatar da kasafin kudin hukumarsa na shekarar 2019/20 a gaban majalisar dokokin kasar.

Irin wadannan masu daukar ma'aikata, wajibi ne su sani cewa, muddin suka karya doka suka dauki baki 'yan ci rani aiki ba bisa ka'ida ba, to za su dandana kudarsu, kuma hukumar bincike ta kasar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen gurfanar da su a gaban shari'a, in ji Bheka.

Ya ce babban dalilin da ya sanya wadansu kamfanoni ke daukar irin wadannan ma'aikata shi ne domin samun riba mai kauri, inda suka zalintar baki 'yan kasashen waje suke biyan su albashi kasa da abin da ya kamata a biya su, saboda sun sani cewa bakin na zaune a kasar ne ba bisa ka'ida ba.

"Ba za mu taba lamintar hakan ya ci gaba da faruwa ba. Za mu yaki da rashawa dake baiwa baki damar shiga kasar ba bisa ka'ida ba," in ji shi.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China