Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Sudan ta kudu na maraba da tsagin adawar kasar da ya shiga aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya
2019-07-11 10:42:05        cri

Shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Kiir, ya ce kofar sa a bude take, ga madugun 'yan tawayen kasar, kuma tsohon mataimakin sa Riek Machar, da ya ziyarci kasar a duk lokacin da yake so domin tattaunawa, da nufin gaggauta aiwatar da yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya, kamar dai yadda kungiyar tarayyar Afirka ta AU ta ba da shawara.

A shekarar bara ne dai sassan biyu, suka sanya hannu kan yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya, wadda ta shafi fannonin da a baya suke takaddama a kan su, a birnin Addis Ababan kasar Habasha.

Da yake yiwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua karin haske game da batun, ministan ma'aikatar watsa labaran kasar Michael Makuei Lueth, ya ce gwamnatin shugaba Salva Kiir, na maraba da zuwan jagoran 'yan tawayen SPLA-IO wato Mr. Machar, domin tattaunawa ta kai tsaye, musamman ganin yadda ya rage watanni hudu kacal, wa'adin kafa gwamnatin rikon kwaryar kasar ya ciki.

To sai dai kuma Mr. Lueth, ya nuna damuwa game da yiwuwar gazawar sassan da ke adawa da gwamnati, na aiwatar da matakan share fagen da aka tsara, amma duk da haka, a cewar sa lokaci bai kure ba, na aiwatar da tantancewa, da tsara rukunonin barikokin sojoji, da kayyade jihohin kasar, da kuma shata kan iyakokin yankunan kabilun kasar.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China