Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta bukaci a dinga sanya ido ta shafin intanet don kawar da ayyukan ta'addanci
2019-07-11 10:03:26        cri

Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta bukaci a tsaurara matakan sanya ido ta shafukan intanet domin dakile ayyukan ta'addanci.

Idriss Mounir Lallali, mataimakin daraktan cibiyar nazarin ayyukan ta'addanci ta Afrika ya bayyanawa dandalin taron kolin AU a Nairobi cewa, gamayyar kungiyoyin ta'addanci suna amfani da shafukan intanet wajen daukar ma'aikata da kuma shirya muggan ayyukan ta'addanci.

"Wajibi ne a sanya ido ga ayyukan ta'addanci ta intanet domin tabbatar da tsaron nahiyar." Lallali, ya bayyana hakan ne a lokacin taron shiyyar Afrika game da yaki da ayyukan ta'addanci da rigakafin hare haren masu tsattsauran ra'ayin addini.

Lallali ya ce, sauran nahiyoyin duniya sun samu nasara wajen yaki da ayyukan ta'addanci ne ta hanyar bibiyar kafofin sada zumunta na zamani, don haka wajibi ne hukumomin tsaron kasashen Afrika su mayar da hankali wajen bibiyar hanyoyin sadarwa na zamani.

"Babban kalubale shi ne yadda za'a binciki shafukan intanet na kamfanonin sadarwa dake gudanar da ayyukansu a wajen kasashen Afrika domin baiwa nahiyar damar tattara shaidun da ake bukata ta intanet don a samu damar hukunta 'yan ta'addana dake shirya munanan ayyuka." in ji jami'in.(Ahmad fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China