Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutanen Sin na sabawa da yin rayuwa ba tare da gurbata muhalli ba
2019-06-03 11:10:29        cri

A karshen makon jiya, cibiyar nazarin manufofin muhalli da tattalin arziki dake karkashin shugabancin ma'aikatar muhallin halittu ta kasar Sin ta kaddamar da rahoton binciken yadda mutanen kasar suke kula da muhallin halittu, wannan shi ne karon farko da aka fitar da alkaluma kan yadda Sinawa suke tafiyar da harkokinsu masu alaka da muhallin halittu. Rahoton ya nuna cewa, an gyara aikace-aikacen da basu dace da tsarin kiyaye muhalli ba, wadanda suka shafi bukukuwan gargajiya da yadda ake zaman rayuwa. Yanzu yin rayuwa ba tare da gurbata muhalli ba ta zama wata halayyar yau da kullum a tsakanin al'ummar kasar Sin.

Rahoton ya ce, galibin al'ummar kasar Sin sun kara sanin yadda za su ba da muhimmanci sosai wajen kiyaye muhallin halittu. Sun dauki matakai a fannonin kiyaye muhallin halittu, da yin tsimin makamashi da albarkatu, da rage gurbata muhalli, da yin zirga zirga ba tare da gurbata muhalli ba, da maida hankali kan kare muhallin halittu. Alal misali, kusan kaso 90 bisa 100 na mutanen da aka tambaye su ba su saya, ko yin amfani, ko cin namun daji da tsirrai, wadanda ba su yi yawa ba a duniyarmu. Fiye da kaso 60 da aka yi musu tambayar su kan yi tafiya da kafa ne, ko hawan keke, ko kuma ta hanyar manyan motoci masu daukar fasinja. Wadannan aikace-aikace masu saukin aikatawa suna da amfani wajen kiyaye muhalli, tare da tsimin kudi, da amfanawa lafiyar mutane. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China