Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan cinikayya tsakanin Sin da Afrika ya karu tsakanin watannin Junairu da Mayu
2019-07-06 16:19:51        cri
Hukumar Kwastam ta kasar Sin, ta ce cinikayya tsakanin kasar Sin da nahiyar Afrika ya dan samu tagomashi a cikin watanni 5 na farkon bana.

Alkaluman da hukumar ta fitar a hukumance, sun nuna yawan cinikayya tsakanin bangarorin biyu ya tsaya kan dala biliyan 84.76 a tsakanin wadancan watannin, adadin da ya samu karuwar kaso 3 cikin dari, idan aka kwatanta da raguwar kaso 1.6 cikin dari da baki dayan cinikayyar kasar Sin da kasashen ketare cikin takardar kudi na dala ta samu a tsakanin wancan lokaci. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China