Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Cinikin kasar Sin ta intanet ya kai yuan tiriliyan 3.86 tsakanin Janairu zuwa Mayu
2019-06-24 09:45:47        cri
Wata kididdigar ayyukan masana'antu ta bayyana cewa cinikin kasar Sin ta intanet ya kai yuan tiriliyan 3.86 kwatankwacin dala biliyan 562 a watanni biyar na farkon wannan shekara, wanda ya kai kashi daya bisa biyar na jimillar kasuwancin kasar Sin baki daya.

Ciniki ta intanet ya kasance a matsayin muhimmin jigon sayayya a shekarar 2019, kamar yadda rahoton ciniki ta intanet na kasar Sin na shekarar 2019 ya bayyana, wanda kwalejin nazarin kimiyya ta kasar Sin (CASS) ta fitar.

Rahoton na CASS ya bayyana cewa, adadin masu yin sayayya ta intanet yana ci gaba da karuwa, yayin da adadin masu sayen kayayyakin ta intanet ya kai miliyan 610 ya zuwa watan Disambar 2018, kana mutane 97 daga cikin mutane 100 suna amfani da wayoyinsu na hannu wajen yin sayayya ta intanet.

A cewar rahoton, darajar kasuwanci ta intanet ya taimaka wajen bunkasuwar kasuwancin kasar Sin da kasashen ketare, inda adadin yawan shigi da ficin kayayyaki ya karu da kashi 50 bisa 100 a shekarar 2018.

A rukunin watannin farko na shekarar 2019, kusan kashi 45.9 na adadin cinikin yuan tiriliyan 1.2 an samu ne ta hanyar kasuwanci ta intanet, Li Yongjian, wani kwararran masanin tattalin arziki na kwalejin CASS ya bayyana hakan. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China