Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kakakin ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ya yi bayani kan kalaman da bangaren Amurka ya bayar
2019-06-05 10:15:33        cri

Kakakin ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ya yi bayani kan tambayar da aka yi masa game da sanarwar da ofishin wakilcin hada hadar cinikayya na Amurka, da ofishin baitulmalin kasar, suka fitar a ranar 3 ga wata, game da "matsayin da kasar Sin ta dauka kan shawarwarin da aka yi tsakanin Sin da Amurka kan takaddamar cinikayya da tattalin arziki" da gwamnatin kasar Sin ta fitar a Lahadin da ta gabata.

Da yake bayanin a jiya Talata, Kakakin ya bayyana cewa, bangaren Amurka ya yi watsi da ka'idojin cinikayya da bangarori daban daban suke bi, ya kuma sha daukar matakan kashin kai da na kare cinikayya bisa hujjar kasancewar dimbin gibin kudin cinikayya, domin tayar da takaddamar tattalin arziki da cinikayya tsakaninsa da kasar Sin. A waje daya kuma, a lokacin da ake shawarwari tsakanin bangarorin 2, a kullum bangaren Amruka na yunkurin tilasta wa bangaren Sin karbar wasu sharudan da zai ci moriya, wadanda a daya bangaren, za su lalata moriyar kasar Sin. Ya ce a bayyane yake cewa, kasar Amurka na nuna halin rashin dattaku.

Kakakin ya ce, a ganin bangaren Sin, dalilai daban daban ne suka haifar da gibin kudi a lokacin da ake cinikayya tsakaninsa da Amurka, kuma shi ne sakamakon karfin kasuwa. Bangaren Amurka ya ci dimbin moriya a cikin cinikayyar da aka yi tsakaninsa da kasar Sin, "ra'ayin cin hasara" ba shi da tushe ko kadan.

Sannan kakakin ya bayyana cewa, a kullum bangaren Sin yana ganin cewa, bangarorin biyu suna bukatar kawar da matsalolin tattalin arziki da cinikayya dake kasancewa tsakaninsu ta hanyar tattaunawa da shawarwari. Ya ce dole ne a yi shawarwari bisa ka'idoji na adalci, da moriyar juna da kuma amincewa da juna. Bangaren Sin na fatan bangaren Amurka ya yi watsi da matakan kuskure, ya tsaya da bangaren Sin kan matsaya guda, kana ya dauki matsayin zaman daidai wa daida, da moriyar juna da kuma amincewa da juna, ta yadda bangarorin biyu za su iya yin watsi da wasu ra'ayoyi mabambanta da kara yin hadin gwiwa domin tabbatar da ganin huldar tattalin arziki da cinikayya tsakaninsu ta samu ci gaba ba tare da tangarda ba kamar yadda ake fata. (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China