Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jagororin wakilan da ke tattauna batun cinikayya da tattalin arziki na kasashen Sin da Amurka sun tattauna ta wayar tarho
2019-06-25 09:46:33        cri
Bisa bukatar Amurka, Mataimakin Firaministan kasar Sin Liu He, ya tattauna ta wayar tarho da Robert Lighthizer, wakilin Amurka dake tattauna batun cinikayya da tattalin arziki da kasar Sin da kuma sakataren baitulmalin Amurkar, Steven Mnuchin.

Bangarorin biyu sun yi musayar ra'ayi kan batutuwan da suka shafi tattalin arziki da cinikayya.

Bangarorin biyu sun kuma amince su ci gaba da tuntubar juna.

Liu He, shi kuma mamba ne a hukumar kula da harkokin siyasa ta kwamitin tsakiya na JKS, kana jagoran wakilan kasar Sin dake tattaunawar cinikayya da Amurka. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China