Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: Idan Sin da Amurka suka cimma yarjejeniya, za a soke dukkanin kudin haraji da Amurka ta karawa kayayyakin Sin
2019-07-04 19:33:30        cri
A yau Alhamis ne, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Gao Feng ya bayyana cewa, yanzu tawagogin kasashen Sin da Amurka suna tuntubar juna yadda ya kamata. Ya ce batun kara dora kudin harajin kwastam kan kayayyakin da kasar Sin take sayarwa a Amurka, shi ne mafarin takaddamar tattalin arziki da ciniki a tsakanin kasashen 2.

Don haka idan kasashen 2 sun kai ga cimma yarjejeniya, to ya zama tilas a soke dukkanin kudaden harajin kwastam da Amurka ta karawa hajojin Sin. Sa'an nan kuma, Sin ta kalubalanci Amurka, da ta hanzarta cika alkawarinta na yarda da kamfanoninta su sayar wa kamfanin Huawei kayayyaki. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China