Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ra'ayoyin kuskure 3 na wasu 'yan siyasar Burtaniya kan harkokin yankin Hongkong
2019-07-05 20:10:51        cri

A kwanan baya, bayan lamarin nuna karfin tuwo, inda wasu masu tsattaurar ra'ayi na Hongkong suka kutsa kai har ma suka lalata kayayyakin babban ginin majalisar kafa dokokin yankin Hongkong, abin mamaki shi ne wasu 'yan siyasa na Burtaniya sun fitar da "Sanarwar Tarayya Tsakanin Sin da Burtaniya" wadda ta riga ta zama abin tarihi, inda suka ce za su goyi bayan 'yancin mazauna yankin Hongkong, da bangaren Burtaniya ya nemo musu daga wajen kasar Sin, har ma sun ce, gwamnatin musamman ta yankin Hongkong ba ta da ikon fatattakar masu zanga-zanga bisa hujjar irin wannan matakin nuna karfin tuwo.

Irin wadannan maganganu nasu masu kunshe da kuskure iri iri, tabbas yana mayar da baki fari, suna kuma shiga dumu-dumu harkokin yankin Hongkong, har ma suna goyon bayan laifuffukan da aka yi a fili, da kuma tsoma baki fiye da kima kan harkokin yankin Hongkong, da na cikin gidan kasar Sin, kuma tabbas za su kawo illa ga dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Burtaniya.

Da farko dai, "Sanarwar Tarayya Tsakanin Sin da Burtaniya" wata takardar siyasa ce da bangarorin Sin da Burtaniya suka kulla a shekarar 1984, domin tabbatar da ganin an mayar da ikon mulkin yankin Hongkong ga bangaren Sin lami lafiya, da yadda aka tafiyar da harkokin yankin Hongkong kamar yadda ya kamata, kafin bangaren Burtaniya ya mika wannan iko ga bangaren Sin. Bayan dawowar ikon mulkin yankin Hongkong a hannun gwamnatin kasar Sin a ran 1 ga watan Yulin shekarar 1997, an sauke dukkan nauyi da hakkokin da aka dora wa bangaren Burtaniya a cikin sanarwar gaba daya. Sakamakon haka, wannan sanarwa ta kasance tamkar wata takardar tarihi ce kawai. Bangaren Burtaniya ba shi da ikon mulkin yankin Hongkong, da ikon tafiyar da harkokin yankin da ikon sa ido, balle "hakkin da'a" a yankin. Gwamnatin kasar Sin na tafiyar da ikonta na mulkin yankin Hongkong, bisa "kundin mulkin kasar Sin" da "Babbar doka ta Hongkong".

Amma har yanzu, wasu mutanen Burtaniya ba su son yin watsi da wannan "Sanarwar Tarayya Tsakanin Sin da Burtaniya" wadda ta riga ta zama abin tarihi, har ma sun yi yunkurin sanya "ba za a sauya muhimman ka'idojin da gwamnatin tsakiyar Sin take aiwatarwa a yankin Hongkong ba har na tsawon shekaru 50" a kan wannan sanarwar. Sun ce, har yanzu sanarwar tana da amfani.

A hakika dai, idan ba su san ilmin tarihi da na siyasa ba, to da gangan suke son mayar da baki fari, da kuma shiga dumu-dumu harkokin yankin Hongkong, ta yadda za su iya samun hujjar tsoma baki fiye da kima kan harkokin yankin Hongkong, da na cikin gidan kasar Sin.

Ban da wannan kuma, wasu mutanen dake kasar Burtaniya sun ce, kasar Burtaniya ce ta nemowa jama'ar yankin Hongkong 'yancinsu, har ma sun yada jita-jitar cewa, ba a samu dimokuradiya ta gaske a Hongkong ba bayan komawar yankin kasar Sin. Dangane da hakan, Martin Jacques, wani masani dan kasar Birtaniya, ya ce wannan karya ce da wasu mutanen Birtaniya su kan yi. A hakika jama'ar Hongkong "ko inuwar Dimokuradiya ma ba su taba gani ba" yayin mulkin mallaka da Birtaniya ta yi a yankin Hongkong. Domin kowa ya sani, a lokacin da Birtaniya ke mallakar Hongkong, duk wani gwamnan yankin sai gwamnatin Burtaniya ta nada. Ba a ba jama'ar Hongkong iko na zabar mutum da suke so ba. Sa'an nan babu wani sashen shari'a mai cin gashin kansa. Za a iya cewa sam babu 'yanci da dimokuradiya a Hongkong a lokacin.

Bayan dawowar yankin Hongkong karkashin mulkin gwamnatin tsakiya ta kasar Sin, gwamnatin ta yi kokarin aiwatar da manufofin "kasa daya amma tsarin mulki biyu", da "a bari jama'ar Hongkong su kula da aikin mulki a Hongkong", bisa tsarin mulkin kasar Sin, gami da dokokin Hongkong. Daga bisani jama'ar Hongkong sun fara zama masu gidan Hongkong, tare da samun hakkin dimokuradiya, da 'yanci da ba a taba ganin irinsu a tarihi ba.

Alkaluman da bankin duniya ya gabatar sun nuna cewa, matsayin yankin Hongkong tsakanin yankuna da kasashe na duniya a fannin aikin shari'a, ya hau zuwa matsayi na 11 a shekarar 2015, daga wani matsayi na fiye da 60 da ya samu a shekarar 1996.

Sa'an nan, na uku, gwamnatin yankin Hongkong a wannan karo ta kula da batun da ya shafi aikace-aikacen nuna karfin tuwo bisa dokoki, don haka babu wani kuskure cikin ayyukan da ta yi. Dokokin Hongkong sun ba mazauna yankin damar bayyana ra'ayinsu, da yin zanga-zanga. Amma duk da haka, lokacin da ake amfani da wadannan damammaki, ya kamata a girmama hakkin sauran mutane, da magance haifar da illa ga tsari da oda na al'umma, gami da tsaron jama'a. Kuma bai kamata ba a keta doka, da aikata laifi na nuna karfin tuwo.

Kwanan baya, wasu masu tsattsauran ra'ayi sun kai farmaki ga 'yan sanda, tare da kutsa kai da yin barna a ginin majalisar kafa dokokin yankin. Abubuwan da suka yi ba yin kalami cikin 'yancin kai da kuma yin zanga-zanga cikin ruwan sanyi ba ne, a'a, sun saba wa dokokin HongKong, da lahanta odar zaman al'ummar HongKong, da kuma kawo illa ga babbar moriyar yankin na HongKong. Yadda 'yan sandan HongKong suka hana su nuna karfin tuwo, da kuma gurfanar da su a gaban kotu, shi ne kiyaye mutuncin dokoki a HongKong.

Amma wasu 'yan Birtaniya sun yi amfani da "ma'auni guda 2" kan abin da ya faru a HongKong. Sun shafa kashin kaji kan halaltattun matakan da 'yan sandan HongKong suka dauka, sun ce, 'yan sanda sun murkushe zanga-zangar. Kada su manta da matakan da gwamnatinsu ta dauka yayin da aka yi fashe-fashe, da kone-kone, da buge-buge a birnin London a watan Agustan shekarar 2011, wadanda kusoshin Burtaniya suka kira su laifuffuka, sun kuma yaba wa yadda 'yan sandan wurin suka kama 'yan bore, inda suka ce, 'yan sandan sun kiyaye dokoki da maido da odar zaman al'ummar kasa. Yanzu yayin da dokoki ba su aiki yadda ya kamata a HongKong, 'yan siyasan Burtaniya sun fito a fili domin mara wa masu boren baya. Yadda suka mayar da baki fari, ya bata ran mutane sosai, kana ya bata sunan Burtaniya, wadda ta kan yi shelar tafiyar da harkokin kasa bisa doka.

Shekaru 22 sun wuce. HongKong, yanki ne musamman na kasar Sin, ba wani wurin da Birtaniya ta yi mulkin mallaka ba ne. Harkokin HongKong, harkokin cikin gida ne na kasar Sin, wadanda duk wata kasa, hukuma da mutum ba shi da ikon tsoma baki cikinsu. Kamata ya yi Sin da Burtaniya su raya hulda a tsakaninsu bisa ka'idojin nuna wa juna girmama a fannonin ikon mulkin kasa, cikakkun yankunan kasa da rashin tsoma baki cikin harkokin cikin gida.

Yanzu 'yan Burtaniya dubu 300 suna zaune a HongKong. In an tayar da tarzoma a HongKong, hakan zai kawo illa ga moriyar wadannan 'yan Burtaniya, lamarin da ba a so a gani. Ya kamata 'yan siyasan Burtaniya wadanda suka tsoma baki fiye da kima kan harkokin HongKong su yi koyi da tarihin HongKong, na komawa karkashin shugabancin kasar Sin, su daina kallon duniya kamar 'yan mulkin mallaka, su kula da harkokinsu tukuna. Ba ruwansu da harkokin HongKong na kasar Sin. (Sanusi, Bello, Tasallah)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China