Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jarin kasar Sin ya zama jarin da masu zuba jari na kasa da kasa suka fi son saya
2019-06-21 20:01:23        cri

Bayan an rufe kasuwannin cinikin takardun hannun jari na kasar Sin a yau Juma'a da yamma, kamfanin FTSE Russell, kamfanin sarrafa alkaluman kasuwannin cinikin takardun hannun jari mafi girma na biyu a duk duniya, ya sa alkaluman kasuwar cinikin takardun hannun jari na A na kasar Sin a cikin kwandon alkalumansa.

Wannan sabon albishiri ne da aka samu a kasuwar jari ta kasar Sin bayan da kamfanin MSCI, wato kamfanin sarrafa alkaluman kasuwannin cinikin takardun hannun jari mafi girma a duk duniya, ya kara adadin takardun hannun jari na A na kasar Sin a cikin kwandon alkalumansa a karshen watan Mayun bana. Wadannan matakan da suka dauka sun alamta cewa, ba ma kawai masu zuba jari na kasa da kasa suna kara zuba jari a kasuwar jari ta kasar Sin ba, har ma suna cike da imani ga makomar tattalin arzikin kasar Sin.

A halin da ake ciki yanzu, kasuwar jari ta kasa da kasa ba ta cikin kwanciyar hankali ba, sakamakon tsanantar takaddamar cinikayya. Amma, har yanzu tattalin arzikin kasar Sin na samun ci gaba mai dorewa kamar yadda ake fata. Ana ganin cewa, kasuwar jari ta kasar Sin, inda za a iya ci gaba da samun riba maras hadari sosai. Yanzu, darajar takardun hannun jari na kamfanonin jarin kasar Sin na da arha sosai, wannan ya jawo hankalin masu zuba jari na kasa da kasa matuka. Sakamakon haka, a ganinsu, kasuwar jari ta kasar Sin ta kasance kamar wata tashar ruwa, inda babu guguwar iska.

A halin yanzu, a kasuwannin samar da takardun bashi da hannayen jari, jarin waje ya dauki kaso 2 zuwa 3 bisa dari kawai, al'amarin da ya nuna cewa akwai sauran rina a kaba, dangane da shigar jarin waje kasuwannin cinikin hannayen jarin kasar Sin.

Shigar jarin kasa da kasa cikin hannun jari masu daraja ta A na kasar Sin, na nuna irin yakini, gami da amincewa da ake nunawa kasar, wadda ke kokarin fadada bude kofa ga kasashen waje, da shiga cikin kasuwannin hada-hadar kudi na duniya. Sin ta kara kawar da cikas da ta kafa ga shigar jarin waje cikin kamfanonin takardun hannayen jari na kasar, kana kuma masu zuba jari na duniya suna iya sayen wasu nau'o'in kayan da aka yi alkawarin za'a samu a nan gaba, ciki har da gurbataccen mai, da ma'adinin karfe. Baya ga tsarin hadin kan kasuwannin hannayen jari na Shanghai da Shenzhen gami da Hong Kong, tsarin hadin kan kasuwannin hannayen jari na Shanghai da London ya fara fadada budewa juna kofa. Haka kuma, an kaddamar da kasuwar cinikin takardun hannun jarin kamfanonin kirkiro sabbin fasahohin zamani, wato SSE STAR MARKET. Duk wadannan matakan da aka dauka sun kara imani da amincewar masu zuba jari na kasa da kasa, kan kokarin da kasuwannin hannayen jarin kasar Sin ke yi na kara bude kofa ga kasashen waje.

A waje guda kuma, ya nuna cewa, masu zuba jari na kasashen ketare suna bayyana wani gagarumin hasashe kan makomar ci gaban tattalin arzikin kasar Sin a nan gaba. Tun bayan aka shiga shekarar nan da muke ciki, bisa yanayin tattalin arziki mai sauyawa a cikin gida da waje, kasar Sin ta karfafa daidaiton manufofi, don tabbatar da wasu muhimman alkaluman tattalin arziki suka kai wani matsayin yadda ya kamata, musamman ma saurin karuwar yawan jarin da aka zuba a fannin masana'antun samar da kayayyakin zamani ya fi na dukkan masana'antun kire-kire da kashi 7.5 cikin dari. Ana iya gano cewa, tattalin arzikin kasar Sin na kara samun saurin ci gaba. A cikin rahoton hangen nesa kan tattalin arzikin duniya da kungiyar IMF ta bayar a watan Afrilun bana, aka kara hasashen da ake yi kan ci gaban tattalin arziki da kashi 0.1 cikin dari, hakan ya sanya kasar Sin ta kasance muhimmiyar kasa a fannin tattalin arziki daya tilo da aka kara hasashe kan bunkasuwarta a bana. Kana kamfanin JPMorgan, da bankin HSBC, su ma sun kara hasashensu kan saurin ci gaban tattalin arzikin na kasar Sin daya bayan daya.

Bisa yanayin rashin tabbaci da tattalin arzikin duniya ke ciki, kasar Sin tana ci gaba da bude kofa ga kasashen ketare, da kara habaka hanyoyin shigar da jarin waje a kasar Sin, ta yadda aka karfafa karfin kasuwannin kasar Sin wajen jawo hankulan jarin waje. Yanzu dai jarin kasar Sin ya zama jarin da masu zuba jari na kasa da kasa suka fi son saya. (Sanusi, Murtala, Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China