Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kawar da rashin amincewa domin kafa kyakkyawar makoma ga Asiya har ma ga duk duniya
2019-06-15 22:17:16        cri

A yau Asabar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron koli karo na 5 na matakan hadin kai da amincewar juna na Asiya da aka yi a Dushanbe, fadar mulkin kasar Tajikistan. A cikin jawabin da ya gabatar a yayin taron, shugaba Xi Jinping ya gabatar da ra'ayoyin kasar Sin da matsayin da kasar Sin ke dauka kan yadda kasashen Asiya zasu iya tinkarar kalubaloli cikin hadin gwiwa, da kafa tsarin al'umma mai kyakkyawar makoma ga Asiya baki daya. Jawabinsa ya samu yabo sosai daga shugabannin sauran kasashen Asiya da na kungiyoyin kasa da kasa da na shiyya-shiyya wadanda suka halarci taron.

A jawabinsa, shugaba Xi ya bayyana ra'ayinsa game da kyakkyawar makomar Asiya. Ya ce, idan ana son kafa wata sabuwar nahiyar Asiya inda ake mutuntawa da kuma amincewa juna, kuma ake cikin kwanciyar hankali da samun bunkasuwa, kana ake yin hakuri da juna sannan ake kirkiro sabbin fasahohin zamani cikin hadin gwiwa, ana bukatar kowane bangare ya yi kokari tare, kuma su warware matsalolin rashin amincewar juna da rashin kwanciyar hankali, da rashin wadata da kuma yadda za a iya tafiyar da harkokin yau da kullum kamar yadda ya kamata.

Game da matsalar rashin amincewar juna, Xi Jinping ya nuna cewa, "mutunta juna da amincewar juna, ka'ida ce da ya kamata kowace kasa ta bi a lokacin da suke yin mu'amala da juna," sannan "ya kamata kowace kasa ta mutunta tsarin siyasa da hanyar neman ci gaba da sauran kasashe suka zaba da kansu," dole ne "a yi watsi da tunani na wani bangare daya dake samun riba, ta yadda wani bangare na daban tilas ya yi hasara' da tunanin kare moriyarta kawai." Idan an yi haka, za a iya "kara amincewar juna kan harkokin siyasa, da kuma cimma matsaya daya kan wasu muhimman manufofi a kai a kai."

Game da matsalar rashin kwanciyar hankali, shugaba Xi Jinping ya ce, idan har kasashen nahiyar Asiya na son tabbatar da cikakken tsaro na daukacin kasashen dake nahiyar, to dole ne su nemi shawarwarin juna a maimakon yin jayaya, da sada zumunta maimakon kulla kawance tare da nuna bambanci", sa'an nan su tsaya kan kokarin dakile duk wani nau'in ayyukan ta'addanci, gami da kau da tsattsauran ra'ayi daga tushe. Sa'an nan a ganinsa akwai bukatar tattaunawa tare da kafa wani tsarin tabbatar da tsaro wanda ya dace da yanayi na musamman na nahiyar Asiya ke ciki, don tabbatar da tsaron nahiyar baki daya.

Dangane da matsalar rashin ci gaba, shugaban ya jaddada ra'ayinsa na "samun ci gaba hanya ce da za a bi don daidaita dukkan matsaloli", inda ya yi kira ga bangarori daban daban, da su taimakawa samar da sauki ga ayyukan ciniki da zuba jari, da neman kulla wasu yarjejeniyoyi irinta "Yarjejeniyar Huldar Abota Da Ta Shafi Dukkan Fannonin Tattalin Arziki A Shiyyar Da Ake Ciki" tun da wuri. Shugaban kasar Sin ya ce kasarsa za ta kara kokarin hada kai da sauran kasashe a fannin manyan tsare-tsare na raya kasa, ta hanyar shawararta ta "Ziri Daya da Hanya Daya", ta yadda za a "sa kaimi ga cikakkiyar hadewar kasashe daban daban, da raya tattalin arziki mai inganci."

Ban da haka, a game da matsalar a fannin kula da al'amuran duniya, wadda aka samu ne sakamakon ra'ayoyi na kashin kai, da kare kai ba tare da kima ba, da kin dunkulewar duniya, shugaban na kasar Sin ya yi kira ga kasashe daban daban da su rike wasu ra'ayoyi masu dacewa, wadanda suka shafi zaman daidaituwa, da koyi da juna, da shawarwari, gami da hakuri da juna. Sa'an nan ya kamata a karfafa cudanya a fannin al'adu, da neman sanya al'adu daban daban kasancewa tare cikin lumana, da yin cudanya da juna, da neman samun ci gaba tare, a maimakon nuna girman kai, da samun takaddama tsakanin al'adu, da wariyarsu, da kuma haddasa dakile cigabansu. A cewar shugaba Xi Jinping, dole a canza don dacewa da zamanin da muke ciki, kana dole ne a yi kokarin kawo sauye-sauye, gami da samar da sabbin fasahohi. (Sanusi Chen, Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China