Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: Kada wasu 'yan Birtaniya sun yi magana ta kuskure kan yankin Hong Kong
2019-07-05 14:11:45        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Mista Geng Shuang ya bayyana matsayin Sin a jiya Alhamis, kan maganar da firaministar kasar Birtaniya ta yi kan batun yankin Hongkong, na cewa, Sin na fatan wasu 'yan Birtaniya kada su yi magana ba bisa gaskiya ba.

A gun taron manema labarai da aka yi a wannan rana, an tambayi ra'ayin kasar Sin game da furucin firaministar kasar Birtaniya Theresa Mary May, inda take cewa, "haddadiyar sanarwa tsakani Sin da Birtaniya ta yi tanadin cewa, ya kamata a mutunta ikon yankin Hongkong na gudanar da harkoki da kansa da 'yancinsa. kuma ita ma tana mai da hankali sosai kan matsalar da Hongkong ke gamuwa da ita."

Mista Geng ya mai da martani cewa, Sin ta mai da martani a kan maganar kuskure ta Jeremy Hunt, ministan harkokin wajen Birtaniya, wanda ya tsoma baki cikin harkokin Hongkong, martanin da kuma ya dace a mai da shi a kan irin wannan furucin da sauran jami'an gwamnatin Birtaniya suka yi. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China