Shanghai zai ci gaba da kasancewa daya daga cikin wuraren da kamfanonin kasashen waje suka fi son zuba jari
Magajin garin birnin Shanghai Ying Yong ya bayyana a jiya a nan birnin Beijing cewa, an tsara shirin raya sabon yankin gwajin ciniki cikin 'yanci a birnin Shanghai, yanzu ana kokarin neman samun iznin gudanar da shi. An gama aikin gina kamfanin Tesla dake birnin Shanghai, za a fara kera motoci a karshen bana. Manyan kamfanoni fiye da 250 na duniya sun tabbatar da halartar bikin baje koli na kayayyakin da aka shigar da su a kasar Sin karo na biyu. An kafa tsarin bude kofa ga kasashen waje mai inganci a birnin Shanghai, za a kara yin kwaskwarima da bude kofa ga kasashen waje a birnin, wanda zai ci gaba da kasancewa daya daga cikin wuraren da kamfanonin kasashen waje suka fi son zuba jari.
Ying Yong ya bayyana hakan a gun taron manema labaru na ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya kuma jaddada da cewa, bude kofa ga kasashen waje shi ne fifikon birnin Shanghai. (Zainab)