Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An rufe taron dandalin tattaunawar Davos na lokacin zafi karo na 13 a Dalian
2019-07-03 19:55:04        cri

A Yau Laraba 3 ga watan nan ne aka rufe taron dandalin tattaunawar Davos na lokacin zafi karo na 13 a birnin Dalian da ke arewacin kasar Sin, bayan da aka kammala ajandar ayyukan da aka tsara baki daya.

Makomar kasar Sin ta fuskar tattalin arziki, da sabbin manufofin Sin kan kamfanonin kasashen ketare, da sauran batutuwan da suka shafi kasar Sin, sun ja hankali sosai a yayin taron. Kana kuma yadda kasar Sin ta shirya kara bude kofa ga ketare, da kuma tsayawa kan yin gyare-gyare a gida, ya samu amincewa sosai.

Yawancin mahalarta taron sun nuna karfin zuciya, da fatan alheri kan yadda kasar Sin za ta kara azama, wajen raya tattalin arzikin duniya da kuma shawararta. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China