Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manzon MDD: Libya na daf da fadawa yakin basasa
2019-05-22 11:10:54        cri

Wakilin musamman na babban sakataren MDD mai kula da kasar Libya Ghassan Salame, ya yi gargadin cewa, kasar Libya na daf da fadawa yakin basasan da zai kai ga raba kan al'ummar kasar.

Jami'in na MDD wanda ya bayyana hakan ga taron kwamitin sulhu na MDD, ya ce, yanzu haka ma sai an dauki shekaru kafin a kai ga daidaita illar da matsalar ta haifar, idan ma an yi nasarar kawo karshen yakin dake faruwa a kasar yanzu haka.

Ya ce, ya shafe kusan shekaru biyu yana kokarin ganin hakan bai faru ba, kamar yadda ya bayyana cikin rahoton da ya gabatar game da halin da ake ciki a kasar. Ya ce, mutane da dama sun mutu baya ga kayayyakin da aka lalata, kwanaki 48 kafin harin da dakarun janar Haftar suka kai birnin Tripoli.

Salame ya ce, yanzu haka, ana iya ganin sakamako da hadarin wannan tashin hankali , musamman yadda al'umma kasar Libya sama da 460 suka rasa rayukansu, kuma 29 daga cikinsu fararen hula ne, baya ga sama da mutane 2,400 da suka jikkata, galibinsu fararen hula, ga kuma sama da mutane 75, 000 da aka tilasta musu barin muhallansu, dukkansu fararen hula. Sama da rabin adadin wadanda suka bar muhallansu mata ne da kananan yara.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China