![]() |
|
2019-06-10 11:07:02 cri |
Sanarwar ta ce, UNICEF za ta yi kokari tare da sassan ba da ilimi na Libya don samar da taimako ga daliban kasar.
Sojojin LNA dake karkashin jagorancin Khalifa Haftar sun fara daukar matakan soja a birnin Tripoli tun daga ranar 4 ga watan Afrilu, inda suka yi musanyar wuta da sojojin GNA wadanda ke da iko a Tripolin. Bisa alkaluman da ofishin hukumar WHO dake Libya ya bayar, an ce tun bayan barkewar fadan tsakanin bangarorin biyu, akwai mutane sama da 600 wadanda suka mutu yayin da wasu sama da 3000 suka samu raunuka, al'amarin da ya sa mutane sama da dubu 60 suka bar muhallansu.
Tun bayan kifar da gwamnatin Muammar al-Gaddafi a shekara ta 2011, Libya ta tsunduma cikin tashe-tashen hankula.(Murtala Zhang)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China