Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin saman Libya dake gabashi sun kai hari kan dakin ajiyar sojoji a Tripoli sun kashe mutane 9
2019-06-16 17:19:44        cri
Mayakan sojojin saman gwamnatin Libya dake da sansaninta a gabashin kasar sun kaddamar da hari kan gidan ajiyar sojojin gwamnatin Libya wanda ke samun goyon bayan MDD a yankin gabashin babban birnin kasar Tripoli, inda suka hallaka mutane 9, kana suka lalata wani asibiti dake kusa da wajen, hukumomi sun tabbatar da faruwar lamarin.

Dukkan mutanen 9 fararen hula ne, sun hada mata 2 da karamin yaro 1, kamar yadda kakakin hukumar lafiyar kasar Fawzi Wanis ya tabbatar.

Sojojin sun ce an shirya kai harin ta jiragen sama ne da nufin tarwatsa dakin ajiyar albarusai mafi girma mallakar dakarun gwamnatin.

Dakarun sojoji, karkashin jagorancin Khalifa Haftar, sun sha kaddamar da hare haren soji tun a farkon watan Afrilu da nufin kwace ikon birnin Tripoli, inda gwamnatin dake samun goyon bayan MDD ke da sansaninta.

A cewar hukumar lafiya ta duniya (WHO), kawo yanzu, fadan yayi sanadiyyar hallaka mutane 653 da kuma jikkata wasu mutanen 3,547.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China