![]() |
|
2019-05-26 21:05:27 cri |
"Hukumar WHO a Libya tayi Allah wadai da kashe jami'an lafiyar biyu a ranar Alhamis a Tripoli a lokacin da aka samu barkewar rikicin wanda ya rutsa da motocin daukar marasa lafiya biyu. Kana wasu jami'an dake kula da motoci da dama suka jikkata," in ji WHO a sakonta na twitter.
An lalata motocin daukar marasa lafiyar biyu a kudancin Tripoli a daidai lokacin da suke gaggawar zuwa ceton mutanen da suka jikkata a sakamakon fadan da ya barke, inji WHO.
Dakarun sojojin, wanda Khalifa Haftar ke jagoranta, suna cigaba da daukar matakan soji tun a farkon watan Afrilu a yunkurinsu na neman kwace ikon babban birnin kasar daga hannun gwamnati.
WHO tace kawo yanzu tashin hankalin yayi sanadiyyar mutuwar mutane 510 tare da jikkata wasu mutanen kimanin 2,467.
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China