![]() |
|
2019-05-31 19:06:22 cri |
Kamfanonin da abokan huldar da za su shiga wannan jerin sunaye, sun kunshi kamfanonin waje da kungiyoyi da daidaikun mutane da ba sa martaba dokokin kasuwa, ko wadanda suka karya ka'idojin kwangila, ko suka katse samar da hajojin bukata ga kamfanonin Sin bisa dalilan da ba na cinikayya ba. Sauran sun hada da wadanda suka gurgunta moriyar halal ta kamfanonin Sin.
Mr. Gao ya ce nan gaba kadan, za a fitar da cikakkun bayanai, game da matakan da za a dauka kan irin wadannan kamfanoni.(Saminu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China