in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron MDD ya amince da kudurin baiwa 'yan gudun hijira kariya
2018-12-18 10:02:42 cri

Galibin mambobin MDD sun jefa kuri'un amince da kudurin martaba yarjejeniyar kasa da kasa, ta baiwa 'yan gudun hijira kariya, tare da bunkasa yankunan da ke karbar bakuncin su.

Yarjejeniyar dai na da nufin ragewa kasashe da yankunan dake baiwa 'yan gudun hijira masauki, wani bangare na nauyin ayyukan da suke gudanarwa, ta kuma samu kuri'un amincewa 181 daga mambobin MDDr 193, kana ta gudana 'yan kwanaki bayan da taron MDD na kasar Morocco ya amince da makamanciyar ta game da 'yan gudun hijirar.

Bisa tanajin ta, yarjejeniyar na da burin ragewa kasashen dake daukar nauyin 'yan gudun hijira kusan miliyan 25 a sassan duniya daban daban, kaso 90 bisa dari na nauyin dake wuyan su, tare da samar da karin damammakin zuba jari, domin fadada samar da ababen more rayuwa, da samar da hidima ga 'yan gudun hijirar da masu masaukin su.

Da take tsokaci game da hakan, mataimakiyar babban magatakardar MDD Amina Mohammed, ta yi kira ga al'ummun kasa da kasa, da su gaggauta aiwatar da yarjejeniyar ba da kariya ga 'yan gudun hijira.

Amurka da kasar Hungary na ciki kasashe kalilan da suka jefa kuri'un rashin amincewa da wannan yarjejeniya.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China