Ofishin babban kwamishina mai kula da 'yan gudun hijira na MDD (UNHCR) ya sanar a jiya Alhamis cewa, a daren Larabar da ta gabata an kwashe bakin haure kimanin 159 daga kasar Libya zuwa kasar Nijer.
"Bayan tsarewar da aka yi musu na watanni masu yawa a Libya, a daren jiya, wadansu matasa 'yan kasar Eritrea dake neman mafaka, an kwashe su a jirgin sama a karon farko, inda aka sauke su a jamhuriyar Nijer," in ji hukumar ta UNHCR.
An kwashe masu neman mafakar ne daga sashen da hukumar ke tattara su a birnin Tripoli tun a farkon wannan watan, inda ake samar musu da abinci, muhalli mai tsafta, kiwon lafiya, da gyaran tunaninsu, in ji sanarwar.
Kimanin bakin haure 3,175 aka kwashe su daga Libya zuwa Nijer, Italy da Romania, a cewar hukumar MDDr.(Ahmad Fagam)