Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabannin kasashen Sin da Kazakhstan sun yi alkawarin kyautata hadin gwiwarsu
2019-06-14 11:25:47        cri

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gana da takwaransa na Kazakhstan, Kassym-Jomart Tokayev, a ranar Alhamis, inda suka yi alkawarin kyautata mu'amalar hadin gwiwa domin moriyar al'ummomin kasashen biyu da ma shiyyar baki daya.

An gudanar da tattaunawar ne gabannin taron kolin hadin gwiwar Shanghai wato (SCO), wanda za'a bude a ranar Jumma'a.

Xi ya taya Tokayev murnar lashe zaben shugaban kasar Kazakhstan, kana ya yaba masa bisa gudunmowar da yake baiwa ci gaban dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Ya yabawa gina tubali, ingantacciyar manufa, da kuma ci gaban da ake samu sannu a hankali game da hadin gwiwar shawarar ziri daya da hanya daya tsakanin kasashen biyu, Xi ya bukaci a kara zurfafa hadin gwiwa kan dangantakar tattalin arziki na kan hanyar siliki tsakanin Sin da Kazakhstan da gina hanyar da zata bunkasa tattalin arziki domin cin moriyar jama'ar kasashe biyu da ma shiyyar baki daya.

Tokayev ya taya murnar cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin.

Bunkasa dangantaka da kasar Sin ya kasance muhimmin batu ga tsarin huldar diflomasiyyar kasar Kazakhstan, a cewarsa, matakin zai taimaka wajen bunkasa ci gaban kasarsa, da zaman lafiyar kasar, kana da ci gaban shiyyar, sannan zai kyautata moriyar al'ummomin kasashen biyu.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China