![]() |
|
2019-06-14 11:08:39 cri |
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce a shirye Beijing take, ta hada hannu da New Delhi wajen ingiza raya dangantaka ta kut-da-kut tsakanin bangarorin biyu.
Xi Jinping ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da Firaministan Indiya Narendra Modi gabanin taro na 19 na kungiyar hadin kai ta Shanghai a Bishkek, babban birnin kasar Kyrgyztan.
Shugaba Xi ya bayyana cewa, kasashen Sin da India su ne kasashe biyu masu tasowa dake da yawan jama'ar da suka kai sama da biliyan guda, kuma dukkansu na wani muhimmin mataki na samun ci gaba cikin sauri.
Ya ce hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu ba bunkasa ci gabansu kadai zai yi ba, har ma da ba da gudunmuwa ga zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba a nahiyar Asiya da ma duniya baki daya.
A nasa bangaren, Narendra Modi ya ce, ganawarsa da Xi Jinping a bara a birnin Wuhan ta yi armashi, wanda ya taimaka wajen samar da sabon ci gaba ga dangantakar dake tsakaninsu, yana mai cewa, India za ta yi aiki da kasar Sin wajen kara karfafa musaya da sadarwa a tsakaninsu. (Fa'iza Mustapha)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China