Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Sin ya tashi zuwa Kyrgyzstan da Tajikistan
2019-06-12 19:07:21        cri
A yau Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya tashi daga birnin Beijing, domin ziyartar kasashen Kyrgyzstan da Tajikistan, inda zai gudanar da ziyarar aiki bisa gayyatar shugabannin kasashen biyu.

Ana sa ran shugaba Xi zai samu tarba daga shugaban Kyrgyzstan Sooronbay Jeenbekov, kana zai halarci taro na 19, na shugabannin kasashe mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ko SCO a takaice, taron da zai gudana a birnin Bishkek, fadar mulkin Kyrgyzstan.

Har ila yau bisa gayyatar shugaban kasar Tajikistan Emomali Rahmon, Xi zai gudanar da ziyarar aiki a hukumance, tare da halartar taro na 5, na tattauna kan batutuwan da suka jibanci cudanya, da karfafa amincewa da juna tsakanin kasashen yankin Asiya, wanda ake wa lakabi da CICA, taron da kuma zai gudana a birnin Dushanbe, fadar mulkin Tajikistan. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China