![]() |
|
2019-06-13 10:42:24 cri |
Shugabannin kasashen biyu sun yi shawarwari kan dadadden zumuncinsu da kyakkyawar makomar dangantakar kasashensu, tare kuma da yin musanyar ra'ayi kan batutuwan da suka jawo hankalin dukkanninsu.
Shugaba Xi Jinping ya ce, hadin-gwiwar Sin da Kyrgyzstan ta fannin shawarar "ziri daya da hanya daya" na ci gaba da inganta. Sin tana fatan yin kokari tare da Kyrgyzstan don kara bunkasa dangantakarsu ta abokantaka bisa manyan tsare-tsare kuma daga dukkanin fannoni, ta yadda jama'arsu za su kara cin moriya.
A nasa bangaren, shugaba Sooronbay Zheenbekov na kasar Kyrgyzstan ya ce, kasarsa na maida hankali sosai kan muhimmiyar rawar da kasar Sin ke takawa a harkokin duniya, kana tana fatan zurfafa hadin-gwiwa tare da kasar Sin ta bangaren "ziri daya da hanya daya", da samun damar cin gajiyar habakar tattalin arzikin Sin, ta yadda dangantakar kasashen biyu za ta bunkasa cikin sauri.(Murtala Zhang)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China