Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya taya murnar bude taron dandalin tattaunawa kan kiwon lafiya na duniya
2019-06-11 14:03:49        cri
An bude taron dandalin tattaunawa kan kiwon lafiya na duniya na dandalin tattaunawa na Asiya na Boao a birnin Qingdao na kasar Sin a yau, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika da wasikar taya murnar bude taron.

Shugaba Xi ya jaddada a cikin wasikar cewa, lafiyar kowane mutum shi ne buri iri daya na dan Adam, kana shi ne muhimmin jigo na raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama. Sa kaimi ga raya sha'anin kiwon lafiya na duniya shi ne kashi bayan ajendar samun bunkasuwa mai dorewa a shekarar 2030. Dandalin tattaunawa na Asiya na Boao ya yi kokarin sa kaimi ga samun bunkasuwa tare da kawo moriya ga jama'a a Asiya har ma ga dukkan duniya, kuma gudanar da taron a wannan karo shi ne muhimmin aiki da dandalin tattaunawar ke yi a wannan fanni. Yana fatan za a cimma daidaito a tsakanin bangarori daban daban da yin mu'amala da juna don sa kaimi ga raya sha'anin kiwon lafiya na duniya da hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa a wannan fanni, yana mai cewa ta hakan za a amfanawa dan Adam a wannan fanni. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China