Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi ya gana da shugaban Rasha a birnin St. Petersburg
2019-06-07 15:45:16        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da takwaran sa na Rasha Vladimir Putin a birnin St. Petersburg a jiya Alhamis. Shugaba Putin ya gayyaci shugaban na Sin zagaye cikin jirgin ruwa a kogin Neva, yana mai maraba da zuwan Xi Jinping mahaifarsa. Kaza lika shugaban na Rasha ya gabatarwa shugaba Xi kayayyakin gargajiya na yankin, da kuma dadaddun gine-gine dake daura da kogin.

Bayan isar su fadar shan iska ta "Winter Palace", shugabannin biyu sun yi musayar ra'ayoyi masu zurfi game da halin da ake ciki, don gane da batutuwan kasa da kasa da na yankuna.

Da yake tsokaci, shugaba Xi ya jaddada cewa, Sin da Rasha suna wani muhimmin matsayi a tarihi, a fannin neman dabarun bunkasuwa, da kara farfado da kasashen su. Ya ce a yanayin da ake ciki, ya dace sassan biyu su zurfafa tsarin su na gudanarwa, ba kawai domin kare moriyar Sin da Rasha kadai ba, har ma da kare hurumin cudanyar kasa da kasa da adalci, da kuma zaman lafiya, da tsaro, da daidaito a sassan duniya.

A nasa tsokaci kuwa, shugaba Putin cewa ya yi, gwargwadon tsanantar yanayi, da zafafar alakar kasa da kasa, gwargwadon yadda Sin da Rasha ya dace su kara zurfafa amincewa da juna ta fuskar siyasa, su kara bunkasa tsarin gudanarwarsu, da hadin gwiwa a harkokin kasa da kasa, su kuma kara azama wajen kare dokoki, da akidun cudanyar kasa da kasa.(Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China