Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da Rasha sun sanar da kiyaye kwanciyar hankali a duk duniya cikin dogon lokaci tare
2019-06-06 10:27:47        cri

Jiya Laraba ne shugabannin kasashen Sin da Rasha suka daddale sanarwar hadin gwiwa a birnin Moscow, inda suka sanar da kiyaye kwanciyar hankali a duk duniya.

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya ce, a matsayinsu na kasashen dake da kujerun dindindin a kwamitin sulhu na MDD, Sin da Rasha zasu ci gaba da hada kai da kasashen duniya wajen kiyaye tsarin kasa da kasa inda aka mayar da MDD a cibiyar tsarin, tare da mayar da dokokin kasa da kasa a matsayin ka'idoji, zasu kuma kiyaye tsarin yin ciniki a tsakanin sassa daban daban, a kokarin kara karfi cikin duniya mai sarkakiyya, a kokarin bada sabuwar gudummowa wajen raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga 'yan Adam.

A nasa bangaren, shugaba Vladimir Putin na Rasha ya ce, Rasha da Sin zasu ci gaba da kara taimakawa juna a al'amuran kasa da kasa da na shiyya-shiyya, wajen daidaita kalubalen ra'ayin bada kariya da ra'ayin daukar matakin gashin kai, da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China