Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da Rasha sun amince da daga matsayin dangantakar su domin sabon zamani
2019-06-05 21:56:25        cri
Kasashen Sin da Rasha, sun amince da daga matsayin cikakkiyar dangantakar su bisa matsayin koli a dukkanin fannoni, ta yadda za ta dace da sabon zamani na gaba. Shugabannin kasashen biyu, Xi Jinping na Sin, da takwaran sa na Rasha Vladimir Putin ne suka cimma wannan matsaya.

Yayin cimma wannan matsaya, shugaba Xi Jinping ya ce, a bana ake cika shekaru 70 tun bayan kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Rasha. Kuma cikin wadannan shekaru 70, an cimma babbar nasara, tare da sanya danba na shiga sabon mataki. Ya ce musamman ma a wannan lokaci da ake fuskantar sauye sauye, Sin da Rasha na dauke da nauyin cimma muhimman nasarori a kasashen su, da ma tsakanin sauran kasashen duniya. Don haka a cewar shugaban na Sin, matakin bunkasa kawance sassan biyu ba shi da iyaka, kuma kasashen na ci gaba da samun nasarori.

Xi ya kara da cewa, Sin a shirye take ta yi aiki kafada da kafada da Rasha, a fannin yayata kyakkyawan tasiri na alakar diflomasiyar dake wakana tsakanin su, tare da ci gaba da sanya al'ummun kasashen biyu, samun nutsuwa a fannin mu'amalar su, da kara ba da gudunmawa ga ci gaban tasirin Sin da Rasha a mataki na cudanyar kasa da kasa.

A nasa bangare kuwa, shugaba Putin cewa ya yi, ziyarar da shugaba Xi ke yi a kasar sa na da matukar alfanu ga alakar kasashen. Ya ce karkashin kwazon sassan biyu, alakar Sin da Rasha ta daga zuwa wani muhimmin matsayi, ta kuma haifar da alfanu ga al'ummun su baki daya.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China