Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da Rasha zasu raya huldarsu daga dukkan fannoni
2019-06-06 09:40:59        cri
A jiya Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Rasha, Vladimir Putin, sun yi zantawa a birnin Moscow na kasar Rasha, inda suka cimma ra'ayi daya wajen tsayawa kan manufar zama cikin jituwa a tsakanin kasashen biyu dake makwabtaka da juna, da kara dankon zumunci, da hadin gwiwa don amfanawa kasashen biyu. Sa'an nan shugabannin 2 sun yi alkawarin cewa, zasu kara kyautata huldar dake tsakanin kasashen 2 a sabon zamanin da ake ciki, don ta zama abokantaka da ta shafi hadin gwiwar bangarorin 2 bisa manyan tsare-tsare na dukkan fannoni. Ta wannan hanya ana neman haifar da karin moriya ga jama'ar kasashen 2, gami da jama'ar duniya baki daya.

Bayan tattaunawarsu, shugabanin kasashen Sin da Rasha sun sa hannu kan sanarwar kara kyautata huldar dake tsakanin kasashen 2, inda aka dora karin muhimmanci da sabuwar ma'ana kan wannan hulda, a shekarar da muke ciki, wadda ita ce zagayowar shekara ta 70 bayan da kasashen 2 suka kulla huldar diplomasiyya. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China