Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Karfafa dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha zabi ne da kasashen biyu ke tsayawa a kai
2019-06-06 09:08:55        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce, karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Rasha, bukatun kasashen biyu ne dake akwai, kuma zabi ne da bangarorin biyu ke tsayawa a kai bisa manyan tsare-tsare.

Xi ya bayyana haka ne a yayin ganawar dake tsakaninsa da takwaransa na Rasha Vlładimir Putin a jiya Laraba a Moscow, inda ya bayyana cewa, ya kamata kasashen biyu su kara mu'amala da hadin kai bisa manyan tsare-tsare, da kuma kara nuna goyon baya ga juna kan wasu muhimman batutuwan dake shafar moriyarsu. Kana ya kamata a sa kaimi kan karfafa hadin kan tattalin arziki da cinikayya a dukkan fannoni, da kuma inganta hadin kan shawarar "Ziri daya da hanya daya" da kawancen tattalin arziki na Turai da Asiya.

A nasa bangaren, Putin ya bayyana cewa, kasarsa na son samar da isasshen man fetur da iskar gas ga kasar Sin, da kara fitar da wasu kayayyakin aikin gona, ciki har da wake da dai sauransu ga kasar Sin, tare kuma da gaggauta hadin kan kawancen tattalin arziki na Turai da Asiya da shawarar "Ziri daya da hanya daya." (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China